Ɗan majalisar dattawa daga jam’iyya mai mulki ta APC, Sanata Kabiru Gaya, ya ce ya kamata jam’iyyarsu ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga yankin kudancin kasar, kamar yadda aka yi alkawari a baya.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya ce, bai wa yankin kudanci takarar shi ne babban alheri da adalci ga APC, kuma a cewarsa zai sa ta ci zabe a shekarar 2023.
Wannan na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa, ana zaman dar-dar a jam’iyyar ta APC gabanin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya tara gwamnonin jam’iyyarsu, tare da shaida musu cewa ya zabi wanda zai gaje shi kuma yana son su goya masa baya.
Sai dai rahotanni sun ce wadannan kalamai ba su yi wa wasu gwamnonin dadi ba.
A tattaunawa da BBC Hausa, Sanata Gaya ya ce: “Ita siyasa, ko ma duk rayuwar duniya, alkawari ce. Idan ka yi wa dan Adam alkawari, to ka cika alkawarin da ka yi da shi. An yi alkawari da kudu cewa su amince Buhari ya yi mulkin shekara takwas, ya kamata kuma a mika musu, domin su ma su yi shekara takwas.”