Adadin mutanen da suka mutu a wani hari kan gidan rawa a Rasha sun kai 133, a cewar wani kwamitin bincike a Rasha.
Yayin da tawagogin agaji ke ci gaba da aikin kwashe ɓaraguzai a wajen da lamarin ya faru, an ci gaba da gano ƙarin gawawwaki, in ji kwamitin a wata sanarwa da ya fitar a dandalin Telegram.
Shugaba Vladamir Putin ya kwatanta harin da aka kai gidan rawan a matsayin “abin tur da kuma aikin ta’addanci”.
“Makiya ba za su raba kan mu ba,” in ji Putin.
Ya kuma gode wa likitoci da jami’an tsaro waɗanda suka taimakawa mutanen da harin na Moscow ya rutsa da su. In ji BBC.


 

 
 