fidelitybank

Adadin mutanen da suka rasu a titin Kaduna zuwa Abuja ya karu zuwa 18 – FRSC

Date:

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC reshen jihar Kaduna, ta ce adadin wadanda suka mutu a hatsarin motan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ya karu zuwa 18, tare da jikkata wasu 27.

Mista Kabir Nadabo, Kwamandan sashin ne ya tabbatar da hakan a wani karin bayani ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Da sanyin safiyar Lahadin da ta gabata ne dai rundunar ta tabbatar da cewa mutane 16 ne suka mutu sannan wasu 27 suka samu raunuka sakamakon afkuwar lamarin.

A cewar Nadabo, hadarin ya faru ne da karfe 05:20 na safe a kan babbar hanyar da ke kusa da unguwar Audu Jangon.

Ya bayyana cewa, abubuwan da suka haddasa hadarin sun hada da gudu da kuma yawan lodin kaya da fasinjoji, lamarin da ya yi sanadin yawan wadanda abin ya shafa.

“Binciken da muka gudanar a kan lamarin ya nuna cewa mutane 65 ne suka shiga cikin hatsarin, 27 sun samu raunuka, 18 kuma sun mutu,” in ji Nadabo.

A cewarsa, rundunar ta Corps Marshal na FRSC ta samar da wasu tsare-tsare a fadin kasar nan a shekarun baya-bayan nan domin tabbatar da daukar matakan gaggawa kan hadurran ababen hawa, musamman a muhimman hanyoyin kasar nan.

latest news 
in nigeria today 2021 punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp