Adadin Isra’ilawan da suka mutu a wajen wani bikin kiɗa ya kai 260, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Isra’ila ke rawaitowa.
Kimanin mutum 3,000 ne suka halarci shagalin wanda Hamas ta ɗana wa tarko da mummunan hari.
An yi shagalin ne a hamadar Negev, kusa da Kibbutz Re’im wanda ba shi da nisa da Zirin Gaza.