Adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu yanzu haka a gobarar birnin LA, wato Los Angeles ya kai ashirin da huɗu.
Ko da yake an samu ci gaba wajen daƙile gobarar, ƴan kwana-kwana na can na shiryawa tarar gagarumar iska mai ƙarfi ta tsawon kwanaki da ke barazanar dagula al’amura.
Wakiliyar BBC ta ce ta kowanne ɓangare, gabas da yadda kudu da arewa ɓarna ce kawai kake gani a nan inda muke, kuma haka lamarin yake a kowanne ɓangare na birnin Lo Angels.
An ɓullo da matakan gaggawa don taimakawa waɗanda gobarar ta shafa da kuma kare su daga masu zamba da masu fakewa da bala’i wajen tsuga farashi.
An kama mutane da dama da laifin kwasar ganima a wuraren da aka fasa, ciki har da wani mutum da ke sanye da kayan kashe gobara.