Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon da za su taimaka mata a sabuwar kakar wasa ta 2025 zuwa 2026.
Sannan kuma ta sayar da wadansu ƴanƙwallon biyar.
Ga jerin ƴanƙwallon da suka koma Anfield:
Florian Wirtz – a kan £100m daga Bayer Leverkusen (zai iya zama £116m)
Hugo Ekitike – a kan £69m daga Eintracht Frankfurt (zai iya zama £79m)
Milos Kerkez – a kan £40m daga Bournemouth
Jeremie Frimpong – a kan £29.5m daga Bayer Leverkusen
Giorgi Mamardashvili – a kan £25m daga Valencia (zai iya zama £29m)
Armin Pecsi – a kan £1.5m daga Puskas Akademia
Freddie Woodman – daga Preston North End
Waɗanda suka bar Anfield:
Luis Diaz – zuwa Bayern Munich a kan £65.5m
Jarell Quansah – zuwa Bayer Leverkusen a kan £30m (zai iya zama £35m)
Caoimhin Kelleher – zuwa Brentford a kan £12.5m (zai iya zama £18m)
Trent Alexander-Arnold – zuwa Real Madrid a kan £8.4m
Nat Phillips – zuwa West Brom a kan £1m (zai iya zama £3m)