fidelitybank

Abun takaici ne ‘yan takara su yi amfani da addini da kabilanci a Kaduna – Hunkuyi

Date:

Sanata Suleiman Hunkuyi, dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kaduna, ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan takara ke amfani da addini da kabilanci wajen jan hankalin jama’a a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Ya kuma caccaki wasu kungiyoyin addini da suka amince da wasu ‘yan takarar gwamna, inda ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan lamari ga makomar dimokradiyya.

Ya ce yin amfani da addini ko kabila a jaha mai sarkakiya kamar Kaduna wajen yakin zabe yana da hadari.

Karanta Wannan: Ku guji siyasar kudi ‘yan Kaduna – Sanata Hunkuyi

Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a ranar Asabar din da ta gabata, dan takarar gwamnan ya shawarci wadanda suka cancanci kada kuri’a da su kaurace wa siyasa mai raba kan jama’a, su zabi sahihin dan takara da zai ciyar da jihar gaba a dukkanin bangarori na rayuwa.

Ya yi bayanin cewa ya yi imani da gwamnatin da ta kunshi kowa da kowa, ba tare da la’akari da shekaru, addini da kabila ba idan aka zabe shi a matsayin gwamna, yana mai jaddada cewa ita ce kadai hanyar da za a tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar.

A cewarsa, “Ina jin kuna sane da wata wasikar da shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Jihar Kaduna ya rubuta, wadda ta amince da dan takarar gwamnan PDP. Muna kuma da wani faifan sauti inda wasu malaman addinin Musulunci suma suka amince da dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamna a jihar Kaduna.”

Ya yi mamakin inda jama’a za su dosa a lokacin da gwamnan da zai fito bayan zabe za a yi wa lakabi da gwamnan kiristoci ko na musulmi a wata babbar jiha kamar Kaduna.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp