fidelitybank

Abun takaici ne yadda Sojoji suka yi mana kutse suka kwato dan uwansu – EFCC

Date:

Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa ta EFCC, ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami’an sojin saman ƙasar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato ‘yan uwansu da hukumar ta tare bisa zargin ‘karya dokar aikin tsaro’.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun jami’ain hulɗa da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba jami’an EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke birnin Kaduna

Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida – da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu – waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen.

”Daga nan ne kuma aka kama su tare da tsare su a ofishin hukumar, bisa zargin karya dokar aiki tsaro”, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

A yayin da ake tare da mutanen hukumar EFCC ta ce ta tuntuɓi rundunar sojin sama ta ƙasa inda hukumomin biyu ke tattanawa domin warware lamarin.

Dele Oyewale ya ce a ranar Juma’a wasu jami’an sojin sama sun dirar wa ofishin EFCCn da ke Kaduna a cikin shirin faɗa, don tilasta sakin abokan aikin nasu.

“Hukumar EFCC ta yi aiki cikin nutsuwa, inda ta ci gaba da tattaunawa da jagororin rundunar sojin saman, kuma daga ƙarshe aka cimma matsayar sakin sojojin bayan an ɗauki bayansu”, kamar yadda mai magana da yawun EFCCn ya bayyana.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp