Shugaban kungiyar dalibai ta kasa (NANS), Umar Faruk Lawal ya ce, abin takaici ne ganin daliban jami’a suna zaune a gida sama da watanni 6.
Lawal ya bayyana haka ne ta wata sanarwa da aka rabawa DAILY POST da yammacin ranar Asabar.
An gudanar da zaben NANS a wurare biyu daban-daban a Abuja ranar Asabar.
Rahotanni sun ce shugabannin bangarorin biyu sun hada da Umar Faruk Lawal da Usman Umar.
Lawal dalibi ne a Sashin Laburare da Kimiyyar Watsa Labarai na Jami’ar Bayero Kano, yayin da Umar kuma dalibi ne a Jami’ar Tarayya ta Dutse, Jihar Jigawa.
Da yake jawabi bayan fitowar sa, Lawal ya bayyana cewa abin takaici ne yadda dalibai suka zauna a gida tsawon watanni shida sakamakon yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) suka shiga.
Sai dai Lawal ya ce NANS a karkashin jagorancinsa a shirye take ta zama sahihiyar muryar daliban a wannan tattaunawa na kawo karshen yajin aikin ASUU.
Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba NANS da ke karkashin sa za ta hadu da ASUU domin kawo karshen yajin aikin da malaman jami’o’in suka yi na tsawon watanni 7.
Shugaban kungiyar NANS ya kuma yi alkawarin cewa kungiyar ba za ta kara shiga harkokin siyasa ba.


