Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan karuwar rashin tsaro a Najeriya.
Da yake tsokaci kan lokacin da ya ke kan karagar mulki, tsohon shugaban kasar ya ce batun tsaro shi ne babban abin da ya sa a gaba a lokacin gwamnatinsa, inda ya bukaci shugabanin da ke ci a yanzu da su dauki kwararan matakai na yaki da matsalar da ke kara ta’azzara.
Da yake magana a wata ziyara da ya kai Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya gana da Sarkin, Dokta Rilwanu Adamu, Obasanjo ya ce magance matsalar rashin tsaro na bukatar hadin kan shugabannin kananan hukumomi, saboda da yawa masu aikata laifuka suna rayuwa ne a cikin al’umma.
Kalamansa “A lokacin da muke mulki, mun ba da fifiko kan tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin kasar nan. A yanzu, muna buƙatar yin wani abu cikin gaggawa game da wannan.
“Mafi kyawun tsarin tsaro shine aikin ‘yan sandan al’umma domin kowa ya san makwabtansa a cikin al’umma. Da wannan, abu ne mai sauqi a gane muggan qwai.”
“Ina kira ga cibiyoyin gargajiya da su shigo tare da karfafa aikin ‘yan sanda a cikin muhallinsu domin rage yawan aikata laifuka”
“Lokacin da muke yi wa kasa hidima, mun yi komai a dunkule, an yanke shawarar mu tare domin a mai da hankali iri daya. Yayana Ahmed Adamu Mu’azu yana nan zaune kuma zai ba ni shaida. Duk abin da muka samu a lokacin, kokari ne na hadin gwiwa.”
Ya kara da cewa “Muna bukatar zaman lafiya, hadin kai da goyon bayan hadin kai a kasar nan idan har ya zama dole mu ci gaba. Abubuwa na iya sake zama daidai kuma a cikin kasar, abin da ya kamata mu yi shi ne mu hada kai mu yi al’amura tare.”
Tun da farko gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya shaidawa majalisar sarakunan gargajiya cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ziyarci jihar ne domin murnar nasarar da gwamnatinsa ta samu.
Ya kara da cewa, a yayin ziyarar, tsohon shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyuka guda biyu da aka kammala a karkashin gwamnatinsa, da nufin inganta ci gaban jihar da kuma saukaka harkokin sufuri.