Shugaban kungiyar Sanatocin arewacin Najeriya, Sanata Abdul Ningi ya ce yana mamakin yadda har yanzu gwamnati ta kasa kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna ta zarce zuwa Kano.
Cikin wata tattaunawa da BBC sanatan ya ce a lokacin kasafin kudin shekarar 2014 da aka sanya makudan kudade lokacin mulkin shugaba Jonathan, amma aka yi biris da aikin.
Ya ce ya auka a lokacin da Buhari ya zo, za a kammala aiki, amma sai ga shi tsohon shugaban ya kammala wa’adin shekarunsa takwas ba tare da kammala aikin ba.
”Irin wannan hanyar ta Abuja zuwa Kano a ce an kasa yinta sai ka ce an yi wa mutane baki, wanda wannan hanyar ita ce kusan ran matafiya ta motoci a yankin arewacin kasar nan’, in ji sanatan dan jam’iyyar hamayya ta PDP.