fidelitybank

Abun kunya ne ‘yan Najeriya su rinka bin layin karbar abinci – Kukah

Date:

Babban limamin Cocin Katolika ta Sakkwato Matthew Hassan Kukah, ya soki lamirin tsarin da ake bi wajen raba tallafin rage raɗaɗi ga ‘yan Najeriya, ana tsakiyar fama da mawuyacin tsananin rayuwa a ƙasar.

Gwamnatoci a dukkan matakai sun ɓullo da hanyoyin bayar da tallafin rage raɗaɗi, bayan cire tallafin man fetur.

Sai dai, da yake jawabi game da batun tsarin raba tallafin rage raɗaɗi, Bishop Kukah ya ce akasarin mutane ba sa samu. Ya nunar cewa a lokuta masu yawa kaso mai yawa na irin wannan kuɗi, sace su ake yi.

Malamin addinin Kiristan na wannan bayani ne lokacin da yake zantawa da gidan talbijin na Channels.

Ya ce: “Muna buƙatar mu ga wani ƙwaƙƙwaran shiri da gwamnati za ta ɓullo da shi, wanda zai taimaka wajen raba mu da irin wannan bin layi muna karɓar tallafi duk da ba a yaƙi muke yi ba.

“Ina jin tsagwaron zubar da mutunci ne a ga ‘yan Najeriya suna bin layi kullum a cikin rana, suna jiran su karɓi buhun shinkafa, wadda mai yiwuwa ba za ta samu ba, ba kuma don ba a bayar da kuɗin ba, amma sai don sanin cewa duk wanda ya ba da kuɗi a Najeriya daga gwamnatin tarayya yana da masaniyar cewa, wani ƙwaƙƙwaran kaso na kuɗin, a ko da yaushe sacewa ake yi.”

sun news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp