Shugaba Bola Tinubu ya ce abin kunya ne yadda Najeriya ke samar da wutar lantarki mai karfin 4.5GW duk da fadin kasar.
Tinubu ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake kaddamar da wani taro mai mambobi 31 na shugaban kasa kan tattalin arziki a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a Villa Abuja jiya.
Ya jaddada bukatar samar da sabbin hanyoyin magance kalubalen tattalin arzikin kasar.
A cewar Tinubu: ”Muna da kalubalen tsaron makamashi a Najeriya. Ya kamata mu hada hannu wajen inganta harkar man fetur da iskar gas, haka nan kuma mu kara samar da wutar lantarki da rarrabawa a fadin kasar nan.
“Mun kuduri aniyar yin hakan tare da hadin kan ku, hadin gwiwa, da shawarwarinku. A matsayinmu na kasa, abin kunya ne har yanzu muna samar da wutar lantarki mai karfin 4.5GW.
“Dole ne mu kara yawan man da muke hakowa zuwa ganga miliyan biyu (2) a kowace rana a cikin ‘yan watanni masu zuwa kuma mun kuduri aniyar kawar da duk wani shingen shiga zuba jari a bangaren makamashi tare da kara yin gasa.”