Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) UNICEF, ya bayyana watsawa Falasdinawa wasu takardu da Isra’ila ke yi ta sama waɗanda ya kunshi batun ba su shawara kan tserewa daga gidajensu a zirin Gaza a matsayin abin kunya.
Wakilin BBC ya ce “babu wani a Isra’ia da zai iya faɗa wa Falasɗinawa wani wuri da za su je don su tsira, sai dai a tura mutane wajen da babu batun tsira”.
Mataimakin shugaban Hamas, Saleh Al-Arouri, ya ce babu wani sauyi a kan waɗanda aka kama har sai an tabbatar da batun tsagaita wuta na dindindin.
A martanin da ya mayar, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ba za a daina yaƙin ba har sai an kawar da Hamas kwatakwata da kuma dawo da sauran waɗanda aka kama gida


