fidelitybank

Abun da zai faru idan na’urar zabe ta ki aiki – INEC

Date:

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana shirin ko-ta-kwana idan na’urar rajistar masu kada kuri’a, BVAS, ta gaza a rumfunan zabe a lokacin babban zaben 2023.

Mai magana da yawun hukumar ta INEC Festus Okoye ya bayyana cewa hukumar za ta tabbatar da samar da kayayyakin BVAS a kowace rumfar zabe.

Okoye ya ce tuni INEC ta yi tanadin yin amfani da BVAS a rumfunan zabe sama da 176,000 a kasar nan.

Da yake magana da gidan talbijin na Channels, Okoye ya ce: “Kowace unguwannin zabe, za mu samu wasu kayayyakin BVAS da za a tura su cikin gaggawa idan akwai wata matsala ko wani kalubale a kowane rumfunan zabe. Mun kuma horar da ma’aikatan goyan bayan fasaha waɗanda kuma za su iya shiga tsakani idan akwai wani ƙalubale tare da BVAS.

“Amma idan har aka ci gaba da samun tabarbarewar BVAS har zuwa lokacin da za a rufe zabe, dokar zabe ta bukaci da mu yi watsi da kada kuri’a a wannan rumbun zabe sannan mu sake kada kuri’a cikin sa’o’i 24.”

sunnnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa...

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...

Masarutar Rano ta haramta aurar da Yaran da ba su kammala karatun Firamare ba

Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga...

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta...
X whatsapp