Tsohon gwamnan jihar Katsina, Barr Ibrahim Shehu Shema, ya ce rashin adalcin da ka yi masa ne ya sanya shi ficewa daga jam’iyyarsa ta PDP.
Cikin wata tattaunawa da BBC, tsohon gwamnan ya ce ya fice daga jam’iyyar ne tun shekarar da ta gabata, bayan ta dakatar da shi tare da Ayo Fayose da Anyim Pios Ayim ba tare da bayyana musu dalilin hakan ba.
”Amma kuma abin haushin shi ne ni kaÉ—ai ne a ciki aka ce an dakatar da zaÉ“aɓɓun shugabannin jam’iyyar daga mazaÉ“ata”, in ji tsohon gwamnan.
”Kan hakan ne na rubuta takarda zuwa ga Party Chaiman na ce ba a bi Æ™a’ida ba wajen dakatar da ni tare da shugabannin jam’iiyar mazaÉ“ar tawa ba, saboda a matsayina na jigo a jam’iyyar wanda ya taÉ“a riÆ™e mukamin mataimakin jam’iyyar mai kula da jihohin arewa 19, na riÆ™e muÆ™amin shugaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar a lokacin, hasalima ni na bijiro da hanyoyi da dabarun ladabtarwa na jam’iyyar, amma aka wayi gari da dakatar da ni ba tare da bayyana min laifin da na aikata ba”, in ji Shema.
”Shi ya sa a cikin takardar da na rubuta na bayar da wa’adin sa’o’i 48 da cewa a bayyana min laifin da na aikata, ni da zaÉ“aɓɓun shugabannin jam’iyyar na mazaÉ“ar har aka É—auki matakin dakatarwar, idan ba a yi ba to zan fice daga jam’iyyar”, in ji tsohon gwamnan
Toshon gwamnan na Katsina ya ce bayan kwana uku ne sai jam’iyyar ta ce ta janye dakatarwar da ta yi masa tare da Ayo Fayose da Anyim Pios Ayim, amma kuma ban da sauran zaÉ“aɓɓun shugabannin jam’iyyar da aka dakatar É—in ba.
Barister Shema ya ce rashin mayar da su zaÉ“aɓɓun shugannin jam’iyyar mazaÉ“ar ne ya sa ya fice daga jam’iyyar.
A baya-bayan nan ne dai, Shema ya yanki katin jam’iyyar APC a mazaɓarsa ta Shema cikin ƙaramar hukumar Dutsin-ma.
Barr Ibrahim Shehu Shema ya mulki jihar na tsawon wa’adi biyu Æ™arÆ™ashin jam’iyyar ta PDP.