A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatinsa ta rufe iyakokin kasar domin kare manoma.
Buhari ya yi magana ne yayin da Shugaban Bankin Raya Afirka, AfDB, Dr Akinwumi Adesina, ya bayyana cewa bankin ya ware dala biliyan 1.5 na shirin samar da abinci na gaggawa na Afirka don dakile illar rikicin Rasha da Ukraine da ake sa ran zai haifar da matsalar abinci a duniya.
Shugaban wanda ya yi magana a wani taro da shugaban AfDB a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa, Abuja, ya bayyana cewa an samu nasarori da yawa wajen karfafa gwiwar manoman yankin, tun bayan rufe iyakokin kasa shekaru biyu da suka wuce. Sai dai ya yabawa bankin na AfDB da ke shirin tunkarar duk wani mummunan sakamako da zai iya tasowa daga rikicin Rasha da Ukraine ta fuskar samar da abinci.
“Na gode da sanin rauninmu da ƙarfinmu, da kuma tsarawa da yin aiki gaba. “Muna sane da bukatar samar da wadataccen abinci, da kuma karfafa gwiwar manomanmu, shi ya sa muka rufe iyakokinmu kusan shekaru biyu, domin dakile fasa kwauri. Mun samu wani ci gaba,” in ji Shugaban.