Wani jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode, ya ce, dimbin jama’a da suka taru a yakin neman zaben jam’iyyar da aka gudanar a jihar Kano, ya nuna cewa dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter.
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama ya ce Tinubu da Kashim Shettima ba wai sun ci jihar ne kadai ba, har ma sun kame yankin Arewa maso Yamma kuma sun ci zaben shugaban kasa a 2023.
Ya rubuta cewa, “Da abin da ya faru a birnin Kano a jiya ya bayyana a fili cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima ba su kadai suka ci jihar ba, har ma sun kwace yankin Arewa maso Yamma kuma sun ci zaben shugaban kasa a 2023.
“Hakika wannan lokaci ne mai ma’ana a wannan yakin neman zabe kuma a bayyane yake a gare ni cewa Allah yana tare da BAT.”