Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Frank Leboeuf ya yabawa Erik ten Hag saboda hukunta Cristiano Ronaldo da ya yi.
A cewar Leboeuf, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya riga ya yi tunanin ya fi kocin, lura da cewa ko da yaushe dan Portugal din ya kan girgiza da nuna alamun a duk lokacin da ba ya filin wasa.
Ronaldo dai ba a cikin ‘yan wasan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Chelsea a karshen mako a matsayin hukuncin da ya bijire wa kocinsa da kuma rashin mutunta abokan wasansa.
Amma Ten Hag ya sanar a ranar Laraba cewa dan wasan mai shekaru 37 ya koma kungiyar gabanin wasan da za su fafata a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Alhamis.
Leboeuf ya yi imanin cewa kocin dan kasar Holland ya yi rawar gani wajen yanke hukunci ga Ronaldo, inda dan kasar Portugal din ya maimaita irin wannan abu a wasan da Man United ta buga da Rayo.
Tsohon dan wasan na Chelsea ya ce rashin da’a ne dan wasan kwallon kafa irin Ronaldo ya rika yin hakan kuma a koda yaushe yana nunawa duniya yana fushi.
Leboeuf ya shaida wa FairBettingSites cewa “Hakanan rashin kwarewa ne kuma don hakan ya sake faruwa a kan Tottenham, ina tsammanin ba za ku iya yin hakan ba, kuma ya san ainihin abin da yake yi kuma yana so ya nuna wa duniya cewa bai ji dadi ba.”