An gano yaran nan ‘yan Colombia hudu da ke cikin jirgin saman da ya yi hatsari a Dajin Amazon sama da wata ɗaya da ransu.
Yaran ‘yan gida ɗaya – masu shekara 13 da tara da hudu da kuma daya, sun ja hankali sosai a yunƙurin ceto su da gwamman sojoji ke yi a dajin.
“Yaran ne kaɗai suka rayu a hatsarin ƙaramin jirgin lokacin da suke tare da mahaifiyarsu da wasu mutum biyu, wanda ya afku a yankin Caqueta.
Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce labarin gano su ya daɗaɗa ran ‘yan kasar baki ɗaya. In ji BBC.
Mista Petro ya ce yaran na samun kulawa a yanzu haka kuma za su koma gida da zarar an tabbatar suna cikin ƙoshin lafiya.