fidelitybank

Abun a yaba wa gwamnan Osun ne yadda ya bijire kan hana shi zabe – Atiku

Date:

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yaba wa Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke bisa gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar, duk da gwamnatin tarayya da ƴansanda sun buƙaci a dakatar da zaɓen.

Tun da farko dai ministan shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi ne ya yi kira ga gwamnan jihar da ya dakata da zaɓen, domin a cewarsa, wa’adin tsofaffin ƙananan hukumomin bai ƙare ba.

Sannan kuma ƴansanda sun yi gargaɗin cewa a dakata da gudanar da zaɓen saboda hukuncin wata kotu, da kuma bayanin sirri da suka samu kan yiwuwar tayar da hargitsi.

Sai dai alamu sun nuna gwamnan ya yi watsi da gargaɗin, inda mutanen jihar suka fito domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen.

Domin haka ne Atiku ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce, “a daidai lokacin da mutanen jihar Osun suka fito domin kaɗa ƙuri’ar zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi, ina sake kira gare su da gudanar da zaɓen cikin lumana. Shugabannin ƙananan hukumomin su ne ƙashin bayan dimokuraɗiyya saboda kusancinsu ga al’umma.

“Ina yaba wa gwamnan Osun Ademola Adeleke bisa gudanar da zaɓen, sannan ina kira ga jami’an tsaro da masu sanya ido a akwatunan zaɓe su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa.”

besda salary

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp