Mafi yawan sassan duniya sun shiga sabuwar shekara ta 2024, sai dai abubuwan da shekarar mai yiwuwa ta tanadar wa rayuwar al’umma.
Ga wasu jerin abubuwan da ake sa ran za su iya faruwa:
Janairu– Gasar cin Kofin Afirka wadda Ivory Coast za ta karɓi baƙunci, za ta kankama.
Fabrairu– Kamar kullum za mu iya sa ran ganin Sabuwar Shekarar Gargajiya a wasu ƙasashe na faɗin duniya (kamar wadda aka fi sani da sabuwar shekarar al’ummar China)
Maris– Vladimir Putin, mutumin da ya jagoranci Rasha a matsayin firaminista da kuma shugaban ƙasa tun 1999, zai sake tsayawa takara a wa’adi na biyar.
Afrilu– Mutane a Amurka za iya ganin kusufin wata na ƙarshe a ƙasar cikin sama da shekara 20, wanda akan yi shagulgula a Arkansas.
A Afrilu zuwa Mayu muna kuma sa ran ganin babban zaɓen Indiya.
Mayu– Kumbon zuwa duniyar wata na China mai suna Chang’e-6 zai yi ƙoƙarin tattaro sama da kilogram biyu na samfura daga sashen duhu na Wata.
Yuni– Mata biyu za su shiga takarar shugaban ƙasa a Mexico yayin da kuma za a buɗe Gasar cin Kofin Turai na UEFA Euro 2024 a Jamus. Sai Gasar cin Kofin Duniya na wasan Kurket mai taken T20 wanda Amurka za ta karɓi baƙunci.
Yuli– Za a fara wasannin Olympic na birnin Paris.
Agusta– Za a fara gasar tseren mata ta Tours de France a Netherlands kuma a kawo ƙarshe a Faransa.
Oktoba– Rasha za ta karɓi baƙuncin babban taron BRICs a kudu maso yammacin birnin Kazan.
Nuwamba– Ma’aikatan farko na kumbon zuwa duniyar wata a cikin shekara 52, ‘yan sama jannati huɗu za su tafi zuwa sararin wata tsawon kwana goma.
Za a yi zaɓen shugaban ƙasa a Amurka, kuma ga dukkan alamu za a sake fafata takara ne tsakanin Joe Biden da kuma Donald Trump ne. In ji BBC.