A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu, ƙarƙashin jagorancin Barrister Aminu Hussaini ya miƙa rahoton bincikensa ga sakataren gwamnatin jihar.
Wasu daga cikin manyan batutuwan da kwamitin ya gano sun haɗa da:
Kwamishinan ya amince ya tsaya wa mai lefin domin raɗin kansa a ranar 18 ga watan Yulin 2025.
Rantsuwa: Ibrahim Namadi ya yi rantsuwa kan belin a matsayinsa na kwamishina mai ci kuma ya yi alƙawarin cika dukkan sharuɗɗan beli har zuwa ƙarshen shari’ar.
Namadi ya fahimci cewa kwamishina kuma ɗan majalisar zartarwa na jiha ne kawai zai iya tsaya wa wani a harkar shari’ar bisa tanade-tanaden sharuɗɗan kotu.
Namadi bai yi takatsantsan ba: Kwamishinan bai yi takatsantsan ba kafin ya ɗauki wannan matsaya ta tsaya wa wani da ake zargi da laifi da ke fuskantar babbar tuhuma da ta jiɓanci safarar ƙwaya.
Kwamishinan yana da cikakkiyar masaniyar haƙiƙanin girman tuhumar da ake yi wa mutumin da ta jiɓanci safarar ƙwaya.
Namadi ya saɓa dokokin gwamnatin Kano dangane da matsayarta da ke fili ta ƙyamar safarar ƙwaya da ta’ammali da ƙwayar da ɓata matasa da sauran laifuka da suka jiɓance su.
Babu shaidar da ke nuna kwamishinan na da wata alaƙa da wanda ake tuhumar kafin yanzu.
Kwamitin bai samu wata shaidar da ke nuna yin amfani da kuɗi ko wata kadara ba domin jan hankalin kwamishinan kafin ya aikata belin.
Kwamishinan bai ajiye ko kwabo ba na beli ciki kuwa har da naira 5,000,000 da ake magana akai. Wannan kawai yana ƙunshe ne a cikin takardar rantsuwar da wanda ake tuhumar ya rubuta.