An naɗa Abubakar Balarabe Ƙofar Naisa a matsayin mai magana da yawun masarautar Kano.
Sanarwar hakan na ƙunshe a wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji.
Abubakar Balarabe Ƙofar Naisa shi ne babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano a kan kafafen yaɗa labarai.
Kuma zai ci gaba da riƙe matsayin guda biyu kamar yadda sanarwar ta tabbatar.
Kafin hakan, Abubakar Balarabe ya kasance wakilin gidan rediyo Kano a ofishin mataimakin gwamnatin jihar Kano daga bisani ya zama wakilin gidan rediyon a ofishin gwamna.
Abubakar Balarabe ya kasance wanda ya taɓa gabatar da fitaccen shirin Taskar Labarai a rediyo Kano. A cewar Matashiya.


