Shahararren mawakin Najeriya, Peter Okoye na kungiyar P-Square, ya ce, abin takaici ne a wulakanta ofishin shugaban kasa.
Mawakin ya kuma ce duk da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da jamâiyyar All Progressives Congress, APC, ba su taka rawar gani ba, amma hakan bai sa a wulakanta shi ba.
Bayanin hakan na kunshe ne a wani sako da ya fitar ta shafin sa na Twitter da aka tabbatar a ranar Talata.
Ku tuna cewa a kwanakin baya ne wasu mazauna jihar Kano suka kai wa Buhari hari a lokacin da ya kai ziyarar aiki.
Karanta wannan:Â Peter Obi ne mafita a zaÉen 2023 – Peter Okoye
Sai dai Okoye ya yi Allah-wadai da matakin, inda ya ce bai dace ba.
Ya rubuta cewa, âDukkanmu mun yarda cewa shugaba Buhari da jamâiyyar APC sun tabuka abin da bai dace ba amma ba mu yarda da wulakanta shugaban kasa ko ofishin shugaban kasa ba. Wannan abin la’ana ne kwata-kwata!”