fidelitybank

Abin damuwa ne yadda Sojoji su ke yi wa fararen hula lugudan wuta a Zamfara – Sanata Yari

Date:

Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Abdul’aziz Yari Abubakar, ya jajantawa wadanda harin da jirgin sama ya rutsa da su a garin Tungar-Kara da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Hare-haren na sama, wanda rahotanni suka ce an yi niyya ne domin kakkabe ‘yan bindigar da ke tserewa, ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama da ba su ji ba ba su gani ba a kauyen.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Al’mansoor Gusau, Darakta Janar na yada labarai ga Sanata Yari, Sanatan ya bukaci a kwantar da hankula, yayin da ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da yin addu’ar samun sauki cikin gaggawar wadanda suka jikkata.

Sanatan ya yi addu’ar Allah ya karbi marigayin a matsayin shahidai, ya ba su aljannah Firdausi.

Ya kuma yabawa sojoji bisa kokarin da suke yi na magance ‘yan fashin, amma ya bukaci a kara daukar matakan taka tsantsan a ayyukan da za a yi a nan gaba domin hana afkuwar asarar da ba a yi niyya ba.

Sanata Yari ya jaddada fatansa na samun zaman lafiya da ci gaba a jihar Zamfara da ma kasar baki daya.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp