fidelitybank

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Date:

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na musamman a rundunar ƴansandan Najeriya da ke Abuja, Abayomi Shogunle ya bayyana dalilin da ya sa suke cigaba da tsare ɗanfafutika kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar African Action Congress wato ACC a zaɓen shekarar 2023, Omoyele Sowore.

Shogunle ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da masu zanga-zangar neman a saki Sowore a ranar Juma’a a Abuja, inda ya ce cewa Sowore ya ƙi yin jawabi ne a lokacin da ƴansanda suke neman jawabin.

Mutanen sun gudanar da zanga-zangar ne a wasu biranen ƙasar irin su Legas da Abuja da Osun da Oyo, inda suke kira da a gaggauta sakin ɗan gwagwarmayar.

Tun da farko, Babban Sufeto Janar na ƴansandan Najeriya ne ya aika da takardar gayyata ga Sowore zuwa hedkwatar rundunar a Abuja a ranar Laraba domin amsa wasu tambayoyi, amma sai aka tsare shi har zuwa lokacin zanga-zangar.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...
X whatsapp