Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na musamman a rundunar ƴansandan Najeriya da ke Abuja, Abayomi Shogunle ya bayyana dalilin da ya sa suke cigaba da tsare ɗanfafutika kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar African Action Congress wato ACC a zaɓen shekarar 2023, Omoyele Sowore.
Shogunle ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da masu zanga-zangar neman a saki Sowore a ranar Juma’a a Abuja, inda ya ce cewa Sowore ya ƙi yin jawabi ne a lokacin da ƴansanda suke neman jawabin.
Mutanen sun gudanar da zanga-zangar ne a wasu biranen ƙasar irin su Legas da Abuja da Osun da Oyo, inda suke kira da a gaggauta sakin ɗan gwagwarmayar.
Tun da farko, Babban Sufeto Janar na ƴansandan Najeriya ne ya aika da takardar gayyata ga Sowore zuwa hedkwatar rundunar a Abuja a ranar Laraba domin amsa wasu tambayoyi, amma sai aka tsare shi har zuwa lokacin zanga-zangar.