fidelitybank

Abia: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 8 a kasuwar shannu

Date:

Aƙalla mutane takwas ne ‘yan bindiga suka kashe a kasuwar shanu ta jihar Abia da ke Kudu maso Kudancin kasar nan a ranar Talata, kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, Kwamashinan Yaɗa Labarai da Tsare-Tsare, Eze Chikamnayo ya na cewa, an kai harin ne da misalin ƙarfe 11:35 na dare.

“A ranar Talata 15 ga watan Fabarairu da misalin ƙarfe 11:35 na dare, wasu ‘ya bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka afka wa ‘yan kasuwa a Sabuwar Kasuwar Shanu ta Omumauzor da ke Ƙaramar Hukumar Ukwa ta Gabas,” in ji shi cikin wata sanarwa.

An kai harin ne kwana ɗaya kafin komawar jagoran ƙungiyar ‘yan tawaye ta Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, gaban kotu, domin fuskantar tuhuma game da zargin ta’addanci a Abuja babban birnin ƙasar.

Hukumomi na zargin ɓangaren ‘yan bindiga na IPOB mai suna Eastern Security Network (ESN) da kai ire-iren waɗannan hare-hare.

the nation newspaper nigeria today latest

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp