fidelitybank

Abdulsamad ya zama na biyu a jerin masu kudin Najeriya

Date:

Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya zarce fitaccen attajirin nan Mike Adenuga, inda ya zama mutum na biyu mafi arziki a Najeriya.

Mujallar Forbes mai wallafa mutanen da suka fi arziki a duniya, ta ƙiyasta arzikin shugaban kamfanin na BUA, da kimanin dala biliyan 7.2, lamarin da ya sa ya zama na biyu mafi arziki a Najeriya, na huɗu a nahiyar Afirka, wanda kuma ke matsayi na 249 a duniya.

Ana alaƙanta ƙaruwar arzikin attajirin da bunƙasar darajar kamfaninsa wanda ke samar da abinci.

Hannayen jarin kamfanin BUA sun samu bunƙasa da kusan kashi 10 cikin 100, a farkon watan Janairun 2024, lamarin da ya sa jarinsa ya ƙaru da dala biliyan 1.92.

A yanzu AbdusSamad Rabi’u, mai shekara 63, ya zarta Mike Adenuga wanda a yanzu Æ™arfin jarinsa yake dala biliyan 6.6.

Mike Adenuga – mai kamfanin Globacom – ya samu raguwar arziki da dala miliyan 400, kamar yadda mujallar Forbes É—in ta nuna, wanda kuma ya koma matasayi na uku a Najeriya na shida a Afirka, sannan yana mataki na 418 a duniya.

Sai dai har yanzu Aliko Dangote ne ke kan gaba a matsayin wanda ya fi kowa arziki a Najeriya da Afirka.

daily 
post news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp