Gwamna Abba Kabir Yusuf ya garzaya Kotun Kolin Najeriya, don ƙalubalantar hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi ranar 17 ga watan Nuwamba a shari’ar zaɓen gwamnan Kano.
Wata takardar kotu da BBC ta gani mai ɗauke da kwanan watan 29 ga watan Nuwamba, na cewa mai ɗaukaka ƙarar yana ƙalubalantar ɗaukacin hukuncin da kotun ta yanke a Abuja, amma ban da ɓangaren da ya ba shi gaskiya.
A baya ma, jam’iyyar NNPP ta shigar da irin wannan kara a gaban kotun kolin, tana kalubalantar hukuncin karamar kotun a kan zaben gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris.
Takardar kotun ta nuna cewa, Gwamna Abba Kabir na neman kotun – wadda ake yi wa kirari da cewa ‘Daga Ke Sai Allah ya Isa – ta saurari ƙarar da ya ɗaukaka.
Haka zalika, ya nemi ta kori ƙorafin jam’iyyar APC, sannan ta ba da umarnin tabbatar da zaɓen mai ɗaukaka ƙarar a matsayin halastaccen ɗan takarar da ya ci zaɓen gwamnan jihar Kano na 18 ga watan Maris.
Kotun ce damarta ta ƙarshe a shari’ance ta ƙalubalantar jerin rashin nasarar da ya samu a gaban kotuna har guda biyu tun bayan kammala zaɓen wata takwas da suka wuce.
Hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓe da na kotun ɗaukaka ƙara dukkansu, sun bai wa jam’iyyar APC nasara ne, kuma suka umarci hukumar zaɓe ta bai wa ɗan takararta, Nasir Yusuf Gawuna shaidar cin zaɓe.
Abba Kabir Yusuf dai ya gabatar da hujja 28 da yake fatan za su zama madogara a gaban kotun ƙoli.
Daga cikin hujjojin akwai batun cewa ƙaramar kotu ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke game da wani shaida da aka gabatar mai taken PW32, mai suna Dr Aminu Idris Harbau, abin da ya janyo soke ƙuri’unsa 165,616.
Abba Kabir yana cewa hujjar da shaidan ya bayar ba ta iya tabbatar da cewa ƙuri’un ba su da inganci ba.
A cewar takardar ƙarar ƙuri’a 3,936 ne kawai ba su da hannu.
Wata hujjar kuma ta yi magana ne a kan hukuncin da ya ayyana cewa Abba Kabir Yusuf ba ɗan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da ya shiga zaɓen 18 ga watan Maris.
Yana mai da’awar takardar rantsuwa mai tabbatar da ingancin bayanan da ya gabatar wa INEC a kan takararsa da katinsa na zama ɗan jam’iyya, sun isa shaida.


