fidelitybank

Abba ya gabatar da ƙwarya-ƙwaryar kasafin Naira biliyan 24

Date:

Gwamnan jihar Kano ya sake gabatar da wani kwarya-kwaryan kasafin kudi ranar Talata na naira biliyan 24 a gaban majalisar dokokin jihar Kano don neman amincewarta.

Abba Kabir ya gabatar da rokon ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar dokokin jihar, Isma’il Falgore ya karanta a zaman majalisar na yau.

Isma’il Falgore ya ce gwamnan ya nemi amincewar majalisar ne kamar yadda sashe na 122 karamin sashe na (A) da (B) na tsarin mulkin 1999 ya tanada.

Ya ce, “kudurin kwarya-kwaryan kasafin kudin na shekara ta 2023 a karo na byu, ya zama dole saboda wasu dalilai daga ciki har da kudaden da jihar ke sa ran samu daga kwamitin rabon kudade na asusun tarayya da harajin VAT da asusun kula da zaizayar kasa da harajin EMTL da kudaden rance na ayyukan samar da lantarki mai zaman kansa daga Babban Bankin Najeriya da kuma karin kudin shiga na cikin gida”.

Gwamnan ya ce bisa la’akari da wadannan bukatu da kuma muradin aiwatar da wasu muhimman ayyukan raya kasa na gaggawa a cikin jihar, an gabatar da kudurin kasafin kudin a kan bangarorin da suka hadar da biyan kudaden garatuti da naira biliyan hudu.

Akwai kuma kashe naira biliyan 20 a kan manyan ayyuka.

A cewarsa da karin kwarya-kwaryan kasafin kudin naira biliyan 58 da kuma na naira biliyan 24, kasafin kudin jihar Kano na shekara ta 2023 a yanzu ya kai naira biliyan 350.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp