fidelitybank

Abba ya ɗaukaka ƙara mai hujjoji 43 na ƙalubalantar nasarar Gawuna

Date:

Gwamnan Kano, da kotun zaɓen jihar ta soke nasararsa, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa shari’arsa gaban kotun ɗaukaka ƙara, inda yake ƙalubalantar hukuncin na ranar 20 ga watan Satumba.

Wata takardar kotu mai kwanan watan 2 ga watan Oktoban 2023, ta nuna cewa Gwamna Abba Kabir ya zayyana Hukumar zaɓe ta INEC da jam’iyyar APC da kuma jam’iyyarsa ta NNPP, a matsayin waɗanda yake da ƙorafi a kansu.

Mai ƙorafin a cewar takardarn kotun, bai gamsu da hukuncin alƙalan kotun ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay ta yanke ba.

Kotun dai ta soke ƙuri’a 165,633 daga cikin 1,019,602 da aka kaɗa wa Abba Kabir Yusuf a zaɓen 18 ga watan Maris, bisa hujjar cewa ba halattattun ƙuri’u ba ne, saboda ba su da hatimi da kwanan wata.

Don haka, kotun ta ayyana Nasir Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen gwamna, ta kuma umarci hukumar zaɓe ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba Kabir Yusuf tun da farko, sannan ta bai wa Gawuna shaidar nasara.

Sai dai Abba Kabir a yanzu ya ƙalubalanci matakin, inda ya yi iƙirarin cewa hukuncin ƙaramar kotun cike yake da kura-kurai, har ma ya kafa hujjoji guda 43.

Cikin buƙatun da gwamnan na jam’iyyar NNPP ya nema a gaban kotun ɗaukaka ƙara, har da ta neman jingine hukuncin kotun sauraron zaɓen gwamnan Kano, sannan ta kori ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar tun da farko.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp