Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da nada wasu shugabannin hukumomin gwamnati da cibiyoyi daban-daban.
Sanarwar na kunshe ne a wani sako da ya wallafa ta kafafen sada zumunta da aka tabbatar a ranar Litinin.
Yusuf ya ce nade-naden da aka yi sun yi nisa ne domin ganin an samar da ingantaccen gwamnati.
Daga cikin wadanda gwamnan ya nada akwai Hon. Kabiru Getso Haruna, babban sakataren hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Kano; Dr. Aliyu Isa Aliyu, Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano; Dokta Kabiru Ado Zakirai, Babban Sakataren Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (KSSMB); Hon. Alkasim Hussain Wudil, Coordinator, Aliko Dangote Skills Acquisition Centre.
Sauran sun hada da Farouq Abdu Sumaila, Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Shawara ta Jihar Kano; Alh. Umar Shehu Minjibir, Shugaban Hukumar Ma’aikatan Jihar Kano; CP Kabiru Muhammad Gwarzo, Rtd. Darakta Janar na Cibiyar Tsaro ta Kamfanoni ta Jihar Kano, Gabasawa da dai sauransu.
Sanarwar ta kara da cewa, “A kudurinmu na ganin an samar da ingantaccen gwamnati a Kano. Na amince da nadin shugabannin hukumomi da cibiyoyin gwamnati kamar haka:
1. Hon. Kabiru Getso Haruna, Babban Sakataren Hukumar ba da tallafin karatu ta Jihar Kano.
2. Dr. Aliyu Isa Aliyu, Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano.
3. Dr. Kabiru Ado Zakirai, Babban Sakataren Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (KSSMB).
4. Hon. Alkasim Hussain Wudil, Coordinator, Aliko Dangote Skills Acquisition Centre.
5. Farouq Abdu Sumaila, Babban Sakataren Hukumar Ba da Shawara ta Jihar Kano.
6. Alh. Umar Shehu Minjibir, Shugaban Hukumar Ma’aikatan Jihar Kano.
7. CP Kabiru Muhammad Gwarzo, Rtd. Darakta Janar na Cibiyar Tsaro ta Kasuwanci ta Jihar Kano, Gabasawa.
8. Dr. Abdullahi Garba Ali, Darakta, Kano Informatics Institute, Kura.
9. Hajiya Shema’u Aliyu, Darakta, Cibiyar Kula da Baƙi ta Jihar Kano.
10. Dr. Musa Sa’ad Muhammad, Daraktan Cibiyar Wasanni ta Jiha, Karfi.
11. Dr. Abubakar Shehu Minjibir, Daraktan Cibiyar Raya Jarida ta Jihar Kano.
12. Abdullahi S. Abdulkadir, Darakta a Cibiyar sarrafa gonaki ta Jihar Kano, Kadawa.
13. Jazuli Muhammad Bichi, Daraktan Cibiyar Dabbobi ta Jihar Kano, Gargai.
14. Dr. Maigari Indabawa, Daraktan Cibiyar Fina-Finai ta Jihar Kano, Tiga.
15. Kabiru Yusuf, Daraktan Cibiyar Kamun Kifi ta Jihar Kano, Bagauda.
Nadin ya fara aiki nan take. – AKY”