Dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci jami’an tsaro da su kama shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, tare da gurfanar da su gaban kuliya bisa zargin kawo cikas a zaben da ke gudana.
Yusuf wanda ya kada kuri’arsa a mazabar Balarabe Haladu dake unguwar Charanchi, ya shaidawa manema labarai cewa ya fahimci akwai tashin hankali da shugaban jam’iyyar APC ke yi wanda ya dage cewa jam’iyyarsa ce kadai za ta kada kuri’a a mazabar sa.
Ya ce duk wanda aka samu yana tayar da hankali to a gaggauta kama shi a gurfanar da shi a gaban kuliya ko da dan jam’iyyarsa ne.
Karanta Wannan: An samu rahotannin siyen kuri’u a Kano
“Ya kamata a gaggauta kama Abdullahi Abbas tare da gurfanar da shi a gaban kuliya, saboda shirya ‘yan daba don haifar da rashin tabbas da haifar da tashin hankali a sashin zaben sa, wanda ya saba wa dokar zabe,” in ji shi.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar lashe zaben bayan an fitar da sakamakon zaben, inda ya kara da cewa atisayen na gudana cikin kwanciyar hankali a sashinsa.