Kungiyar Kwadago reshen jihar Kano, ta bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf, da ya taimaka wa kungiyar wajen ganin an biya hakin ‘yan fansho, wanda ya kai sama da Naira biliyan 75.
Da yake jawabi yayin faretin ranar bikin ma’aikata ta duniya na bana a ranar Larabar nan.
Kwamrade, Kabiru Inuwa, ya ce, babbar barazana ne ga ‘yan fansho kan rashin kin biyan kudin sun a tsawon shekaru
Ya kuma ce, abun a yaba wa gwamnati mai ci ne, kan fara biyan cikakken kudin ‘yan fanshon, kuma suna bukatar duk hukumomin gwamnati da suka kasa biya, da su fara biyan kudaden su, domin samun damar daidaita albashin ritayar su.
Sai dai ya yi kira da a sake duba batun biyan albashin ma’aikata da aka biya sau daya kawai, yana mai cewa ma’aikata sun dogara da kyaututtukan ne domin inganta rayuwarsu sannan a samar da tsarin biyan albashi mai kyau domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.
Kwamrade Kabiru Inuwa, ya bayyana cewa ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi da ake nema na da matukar muhimmanci ga ci gaban jihar nan.
Da yake jawabi a madadin Gwamnan Jihar, Mataimakin Gwamnan, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce tun lokacin da suka karbi ragamar mulki sun yi kokarin ganin sun samu saukin rayuwa ga ma’aikata, inda ya tunatar da su cewa, cikin kankanin lokaci gwamnati ta biya maia’aikatan da suka yi ritaya sama da Naira Biliyan 6.