fidelitybank

Abba ka tsaya da ƙafafun ka ni dai na fita daga Kwankwasiyya – Sanata Ali Madakin Gini

Date:

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai, Ali Sani Madakin Gini ya tabbatarwa da BBC cewa ya fita daga tsagin Kwankwasiyya a cikin jam’iyyarsa ta NNPP.

Ɗan majalisar mai wakiltar Dala a tsakiyar birnin Kano ya tabbatar da haka ne bayan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda a ciki aka ji yana cewa “Daga yau, na daina harkar Kwankwasiyya”.

A cikin bidiyon Ali Madakin Gini ya bayyana cewa “Kwankwasiyya ƙarya ce, Kwankwasiyya yaudara ce”.

Ya ƙara tabbatarwa da BBC cewa: “Na fahimci cewa an gina tafiyar Kwankwasiyya ce kawai domin ci gaban Kwankwaso”.

Zuwa yanzu dai ba a ji wani martani daga ɓangaren Sanata Kwankwaso ba a kan wannan ikirari.

Shi dai Ali Madaki ya ce har yanzu yana nan a jam’iyyarsa ta NNPP, amma ba tsagin jagorancin Sanata Rabi’u Kwankwaso ba.

Matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano, wanda jam’iyyar NNPP ta lashe dukkan kujerun.

An jiyo Ali Madakin Gini yana yaba wa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da cewa shi mutumin kirki don haka ya shawarce shi da ya yi duk yadda zai yi, ya tsaya da ƙafarsa.

A kwanan baya ne dai wata ƙungiya ta ɓullo a fagen siyasar Kano mai taken ‘Abba Tsaya da Ƙafarka’ mai rajin gwamnan na Kano ya daina biyayya ga jagoran Kwankwasiyya, ya ci gashin kansa, lamarin da ya janyo jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Kano da wani kwamishina, bisa zarginsu da alaƙa da ƙungiyar

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp