Saukar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa daga muƙaminsa na shugaban hukumar Hisbah na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce, inda fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya ya shawarci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nemi afuwar Malam Aminu Daurawa.
Gadon Kaya ya yi wannan kira ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na facebook.
Ya ce “Muna kira ga gwamna Abba Yusuf da waɗanɗa ke kusa da shi su kai zuciya nesa su kira malam Daurawa, su zauna da shi kuma su ba shi haƙuri kan abubuwan da ya faru.”
A safiyar Juma’a ne Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da saukar sa daga muƙamin shugaban Hisbah ta jihar Kano.
Daurawa ya ce ya yi hakan ne bayan wasu kalamai da gwamnan jihar Abba Kabir ya furta a ranar Alhamis, waɗanda suka karya masa gwiwa.
A bidiyon nasa, Sheikh Abdallah Gadon Ƙaya ya ce ya kamata gwamna Abba Yusuf ya duba al’ummar jihar Kano da ci gaban da malam Daurawa ya kawo da kuma gudummawar ya yake bai wa ita gwamnatin ta Kano.
“Ya kamata a zauna da shi malam Daurawa a ba shi shawarwari a kan abubuwan ya yake yi ko ake ta cewa Hisbah take yi.” in ji Gadon Kaya.
“Matsayin malam Daurawa ya kai kuma darajarsa ta kai.”
Gadon Kaya ya ce yana bayar da shawarar ce saboda ci gaban jihar Kano da ci gaban gwantin gaba ɗaya.
Hisbah dai ta riƙa shan suka daga wasu ɓangarori na al’umma bayan da wani faifan bidiyo ya yaɗu a shafukan sada zumunta, inda aka ga jami’an hukumar na jefa wasu matasa da ake zargi da aikata ‘rashin tarbiyya’ cikin mota.
Sai dai ana kallon ajiye aikin Sheikh Daurawa, wanda ɗaya ne daga cikin malamai mafiya shahara a arewacin Najeriya a matsayin koma-baya ga yunƙurin tabbatar da ɗa’a a jihar ta Kano, kuma wani mummunan tabo ga gwamnatin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.