Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris ta kira Donald Trump a waya domin taya shi murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa, a y cewar rahoton kafar yaɗa labarai ta CBS.
Yayin kiran, Kamala ta jaddada batun miƙa mulki cikin lumana, da kuma zama shugaba na kowa da kowa ga Amurkawa, kamar yadda wani mai taimaka mata ya faɗa wa CBS.
Ana sa ran za ta yi wa jama’a jawabi a farfajiyar jami’ar Howard University a yau Laraba.