Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce aƙalla mutum 7,000 ne aka kashe a Gaza tun lokacin da aka fara yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba – wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da 500 tun daga ranar Laraba.
Adadin ya hada da yara sama da 2,900, a cewar ma’aikatar.
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, Isra’ila ta ce ta kai hari ta sama kan wasu wurare 250 na Hamas.


