Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya fice daga kasar nan zuwa kasar waje, domin gudanar da wasu aiyuka na al’umma, Inda ya mika ragamar mulkin Kano ga mataimakinsa kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, kafin dawowarsa.
Gwamna Ganduje ya umarci dukkan ma’aikatu da hukumomin jihar Kano, da su yi aiki tukuru domin taimakawa mukaddashin gwamnan wajen gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu.
“Ina yi masa fatan samun nasara a matsayinsa na mukaddashin gwamna,” a cewar Gwamna Ganduje.
Karanta Wannan: Gwamnoni za su yi kokari na magance yajin aikin ASUU -Ganduje


