Kamfanin hakowa da sarrafa albarkatun man fetur na kasa NNPCL, ya bayyana cewa cikin watan Maris din 2023 ne za a fara aikin hako danyen man fetur a jihar Nassarawa.
Shugaban Kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana hakan a wani sako ta shafin Tuwita, inda ya ce, hakan ci gaba ne da aikin hako mai da nufin samar da rijiyar mai ta farko a jihar ta Arewacin ƙasr nan.
Ya shaida hakan a lokacin da yake karbar bakuncin tawagar fitattun yan asalin jihar ta Nassarawa, karkashin jagorancin Gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule a ofishin kamfanin da ke Abuja, babban birnin kasar.
Gano arzikin man a Nassarawa ya zo ne kusan wata biyar bayan da NNPC ya soma aikin hako mai a yankin Kolmani, da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.
Tun a shekarar 2019 ne kamfanin na NNPC ya bayyana gano albarkatun man fetur a yankin na Kolmani.