Shugaban Ukraine Volodymir Zelensky ya bukaci kasashen duniya su hanzarta wajen tursasa Rasha ta fice daga cibiyar sarrafa nukiliya ta Zaborijja (Zaporizhzhia) da ta mamaye a kudancin kasar.
Zelensky ya ce korar Rasha daga cibiyar zai amfani duniya baki daya, ba Ukraine kadai ba.
Shugaban ya yi wannan kalami ne awowi kadan bayan da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya yi wani zama, sa’ilin da Amurka da China suka bukaci da a bai wa masana damar shiga cibiyar.
Da yake nuna goyon baya ga kalaman shugabansa, jakadan Ukraine a kwamitin tsaron ya ce babu wanda zai iya tare iska idan ta kwaso sanadari masu illa daga cibiyar.
Rasha dai ta ce tana kokarin kare cibiyar ne. In ji BBC.


