fidelitybank

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Date:

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin komawa majalisar ranar Talata mai zuwa duk da dakatarwar da aka yi mata.

Sanatar mai wakiltar mazaɓar jihar Kogi ta Tsakiya ta ce za ta yi hakan bisa hukuncin kotu, wadda ta ce dakatarwar wata sida da majalisar ta yi mata ta saɓa dokar tsarin mulkin Najeriya.

Sai dai majalisar ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, wanda ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafi da ta yi wa Shugaban Majalisa Godswill Akpabio da ɓata suna.

Da take magana da manema labarai a ranar Asabar, Natasha ta ce ba ta dakatar da aiki ba duk da ba ta zuwa zauren majalisar.

“Zan je [majalisar] da yardar Allah a ranar Talata, saboda kotu ta bayar da hukunci kan hakan. Amma suna cewa wai ai matsaya ce kotun ta ɗauka ba umarni ta bayar ba. Amma tsarin mulki ya ce duk wata shawara ko matsaya daga kotu na nufin umarni,” a cewarta.

latest nigeria newstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...
X whatsapp