fidelitybank

A tabbata an kama duk motocin da ba su da lamba a Abuja – ‘Yan sanda

Date:

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar Abuja, ta bayar da umarnin kama duka motoci marasa lamba da ke yawo a faɗin birnin.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Josephine Adeh ta fitar, ta ce kwamishin ‘yan sandan birnin, CP Benneth C. Igweh ne ya bayar da umarnin don kakkaɓe ayyukan ɓata-gari da ke fakewa da tuƙin mota suna cutar da al’umma.

“Rundunar ‘yan sandan birnin Abuja ta damu matuƙa kan yadda ake tuƙa wasu motoci a birnin da lamba ɗaya kacal a jikinsu, da ma waɗanda ba su da lambar har fiye da lokacin da doka ta yarje, wato ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na maraice, kamar yadda sashe na 25 (5) na dokar sufurin birnin Abuja ta 2005 ta tanada”, in ji sanarwar.

‘Yan sandan sun kuma aike da makamancin wannan gargaɗi ga masu sayar da motoci, sannan ta yi kira a gare su don kauce wa ajiye motocinsu a wurin da doka ba ta amince da hakan ba.

Sanarwar ta ce an ɓullo da dokar ce domin kakkaɓe ayyukan ɓata-garin da ke fakewa da hakan wajen cutar da al’umma.

“Ba sabon abu ba ne yadda ake samun matsalar fashi a cikin motocin da aka fi sani da ‘one chance,’ inda galibi ke amfani da motoci marasa lamba ko masu lamba guda wajen aikata laifin. Wannan aika-aika na ci gaba da sanya fargaba a zukatan al’umma, waɗanda ke ci gaba da aza ayar tambaya kan abin da ya sa har yanzu ‘yan sanda suka kasa magance matsalar”, in ji ‘yan sandan.

 

sspdf news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp