Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro da tattara bayanan siri ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta saya wa shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sabbin jiragen sama.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa shawarar kwamitin na kunshe ne a cikin wani rahoto da aka fitar bayan bayan binciken da kwamitin ya gudanar kan halin da jiragen saman fadar shugaban kasa ke ciki a halin yanzu.
Rahoton kwamitin ya nuna buƙatar samun ƙarin jiragen guda biyu, inda ya yi nuni da irin hadurran da ake iya fuskanta sakamakon gazawar aiki na jiragen da ake da su.
“Kwamitin yana da kwakkwaran ra’ayi da sanin ya kamata, idan aka yi la’akari da gurguwar tsarin tarayyar Najeriya tare da sanin irin illar da ke tattare da duk wani hatsaniya da za ta iya tasowa a sakamakon gazawar jiragen saman shugaban kasa.
A watan Mayu, majalisar wakilai ta umarci kwamitin tsaro datattara bayanan siri na kasa da ya gudanar da cikakken bincike kan ingancin jiragen shugaban ƙasa da abubuwan fasaha.
Wannan umarnin ya biyo bayan kudirin da Satomi Ahmed, shugaban kwamitin majalisar ya gabatar.
Kudirin ya haifar da zazzafar muhawara a zauren majalisar, inda wasu ‘yan majalisar suka nuna cewa ya kamata shugaban kasar ya yi tafiya ta hanyar jiragen kasuwanci ko ta hanya.
Ahmed ya gabatar da buƙatar ne sakamakon rahotannin da ba su dace ba a cikin jiragen shugaban kasa, wanda a kwanakin baya ya tilasta wa shugaban kasar yin amfani da jirgin haya daga Netherlands zuwa Saudi Arabiya a lokacin da yake tafiya zuwa kasashen waje.