Taiwo Awoniyi ya kuduri aniyar ci wa Super Eagles kwallo akai-akai.
Dan wasan gaban Nottingham Forest ya zura kwallo daya a wasanni hudu da ya buga wa zakarun Afirka sau uku.
Dan wasan mai shekaru 25 ya zura kwallo a ragar Super Eagles yayin da aka tashi kunnen doki 2-2 a wasan gwaji ranar Juma’a.
Awoniyi ya shaida wa NFF TV cewa “Kowane dan wasan yana son ya zura kwallo a raga saboda aikinku shine zura kwallaye da taimakawa abokan wasan ku.”
Awoniyi ya kuma yi magana kan wasan sada zumunci da kungiyar za ta yi da Desert Foxes.
“Ina ganin zai kasance wasa mai kyau ga kasashen biyu,” in ji shi.
“Algeria kasa ce da ke da kwararrun ‘yan wasa amma a gare mu, wasa ne da zai sa mu kara sanin juna da kuma sa mu mai da hankali kan kalubale na gaba.”