Andrew Wynne, dan kasar Birtaniya, wanda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa yana neman hambarar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu, ya ce ba guduwa ya yi ba.
Ƴan sanda sun bayyana Wynne da wani dan Najeriya, wani Lucky Ehims da ake nema ruwa a jallo, ya ba su kyautar Naira miliyan 20.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Muyuwa Adejo, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce duk wanda ya samu labarin da ya kai ga cafke mutanen biyu, za a ba shi tukuicin Naira miliyan 10 ga kowane daya daga cikin wadanda ake zargin.
Sai dai da yake magana kan lamarin a wani shirin gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, Wynne ya ce a shirye yake ya tattauna da ‘yan sandan Najeriya.
Da yake musanta zargin, dan kasar Birtaniya ya bayyana cewa, ba zai iya yin wata makarkashiya don tada zaune tsaye a shugabancin gwamnatin Najeriyar ba, yana mai cewa ya shafe sama da shekaru 25 yana ziyartar kasar.
Ya bayyana shirin sa na ganawa da jami’an hukumar ta Najeriya a birnin Landan domin tattaunawa kan wannan zargi.
Ya ce, “Ban san cewa ni mai gudu ba ne. Ban san cewa ina guje wa doka ba.
“Na kai ziyara Najeriya tsawon shekaru 25 kuma na yi kantin sayar da littattafai a ofishin NLC da ke tsakiyar Abuja tsawon shekaru bakwai. A duk tsawon lokacin, tabbas jami’an tsaro ba su biya ni ba.
“Na fi farin cikin yin magana da ‘yan sanda da tattaunawa ta WhatsApp ko Zoom.
“Na fi farin cikin zuwa Landan na gana da jami’ai a babban hukumar Najeriya a Ingila.”


