Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce a shirye ta ke ta hada kai da sojojin Najeriya wajen yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano.
Hakan ya fito ne daga bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari ranar Alhamis a Kano.
Sanarwar ta ce kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, Mista Abubakar Idris-Ahmad, ya bayyana haka a lokacin da sabon kwamandan 3 Brigade na sojojin Najeriya, Birgediya-Janar M. A. Sadiq, ya kai masa ziyarar ban girma.
An ruwaito Idris-Ahmad yana yabawa rundunar sojin bisa wannan ziyarar, inda ya kara da cewa irin wannan hadin gwiwa zai samar da hadin kai, da magance shaye-shayen miyagun kwayoyi, laifuka da kuma tarwatsa iyali.
Hukumar, a cewarsa, tare da hadin gwiwar rundunar Sojoji, za su samar da cikakkiyar dabara don kare jihar daga illar shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Don haka ya bukaci kungiyoyin raya kasa, masu ruwa da tsaki, al’umma da malaman addini da su marawa hukumar baya a yakin da take yi da wannan annoba.
Da yake mayar da martani, Sadiq ya yabawa hukumar bisa jajircewarta wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.
Ya ce sun kai ziyarar ne domin hada kai da hukumar NDLEA domin magance kalubalen tsaro da ake fama da su a wannan zamani, inda ya kara da cewa, “ana tafka manyan laifuffuka ta hanyar shan miyagun kwayoyi.
“Rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da hada kai da hukumar ta NDLEA a kan musayar bayanan sirri, gudanar da ayyukan hadin gwiwa da kuma shirye-shirye na karfafa gwiwa don magance tushen shaye-shayen miyagun kwayoyi da hana yaduwarsa a jihar,” in ji Sadiq.