Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce ƙasarsa ”a shirye take ta shiga yaƙi”
Da yake jawabi a yayin wata ziyara a Baghdad, Abbas Araghchi ya ce ”Mun shirya tsaf domin fuskantar duk wni yanayin yaƙi. Ba ma tsoron yaƙi ama kuma ba mu son yaƙi, mun fi ƙaunar zaman lafiya”
Ya kuma bayyana cewa Iran ”za ta yi aiki domin wanzar da zaman lafiya a Gaza da kuma Lebanon.”
Ministan hrkokin wajen Iran ɗin ya ziyarci Iraqi ne domin tattauna hanyoyin kawo ƙarshen yaƙi a Lebanon da Gaza.